1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudanin siyasa a Cote d'Ivoire

Abdullahi Tanko Bala GAT
July 9, 2020

Mutuwar firaministan kasar Cote d'Ivoire kana dan takarar jam'iyya mai mulki Amadou Coulibaly ta jefa siyasar kasar a cikin hali na rashin tabbas a yayin da ya rage watanni uku a gudanar da zabuka a kasar.

Amadou Gon Coulibaly | Premierminister der Elfenbeinküste gestorben
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Rasuwar firaministan Cote d'Ivoire Amadou Gon Coulibaly ta ta jefa siyasar kasar cikin halin rashin tabbas yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe cikin watanni uku masu zuwa.

Kafin rasuwarsa Amadou Coulibaly shi ne wanda Shugaban kasar ta Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya tsayar domin yi wa jam'iyyar RHDP mai mulki takarar shugabancin kasa a zaben mai zuwa.

Hoto: AFP/Getty Images/S. Kambou

A halin da ake ciki dai hankula sun karkata ga wanda Jam'iyyar za ta zaba domin maye gurbin Amadou Coulibaly a matsayin dan takara a zaben da ake yi wa kallo a matsayin zakaran gwajin dafi na dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mai arzikin Cocoa.

Firaminista Amadou Gon Coulibaly ya rasu a jiya Laraba yana da shekaru 61 bayan wata 'yar rashin lafiya yayin taron majalisar ministoci.