1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Sarki Douala Manga Bell da ya yi turjiya ga Jamusawa

Fotso Henri ATB/LMJ/MNA
January 7, 2021

Sarki Rudolf Douala Manga Bell da yai karatunsa a Jamus, yana son al'adar Jamusawa. Sai dai daga baya Turawan mukin mallaka na Jamus sun ba shi kunya, lokacin da suka sauya akalar al'ummar kasarsa.

Zeichnung African-Roots-Beitrag

Wane ne Rudolf Douala Manga Bell? 

Rudolf Douala Manga Bell (a kan rubuta Duala) an haife shi a 1873 a Douala. Shi jika ne ga Sarki Ndumbe Lobe Bell — da ake kira Sarki Bell — wanda ya saka hannu kan yarjejeniyar kariya da Daular Jamus a 1884. 

Rudolf Douala Manga Bell ya yi karatu a Jamus kafin komawa kasarsa wato "Kamaru" domin ya taimaki mahaifinsa mulkin masarautar Douala. Ya gaje shi a ranar biyu ga watan Satumba 1908. 

Wani abu ne ya saka Rudolf Douala Manga Bell raba gari da Jamuwasa 'yan mulkin mallaka? 

Bayan samun horo kan dokokin Jamus - wasu majiyoyi sun ce ya yi karatu a Jami'ar Bonn - Sarki Douala Manga ya samu damar aiki da 'yan mulkin mallaka yayin da yake rike da sarauta a kasarsa. Amma ya gaza jure mulkin Jamus. Ya gano Turawan mulkin mallakar na Jamus ba sa mutunta dokokinsu. Bayan shekara biyu ya yi murabus, inda 'yan Douala suka nada shi mai gwagwarmya da Jamusawa 'yan mulkin mallaka wadanda suke kwace musu filaye, abin da Sarkin Douala Manga ya nuna a matsayin karya yarjejeniyar da aka kulla da kakansa. 

A Douala, an banbanta Turawa da bakake 'yan kasa a lokacin. Jamusawa sun nemi kawar da 'yan kasa daga wasu wurare da aka kebe na Turawa, saboda ana zargin bakake da yada zazzabin cizon sauro. 

Yaya Rudolf Douala Manga Bell ya jagoranci gwagwarmaya? 

Rudolf Douala Manga Bell ya sauya dabarun gwagwarmaya wajen neman ganin an yi tawaye. Ya samu masu alaka a daukacin "Kamaru." Gwagwarmayar ta kai har fadar gwamnatin Jamus da suka fahimci al'umma na neman samun cin gashin kai. 

Sarki Rudolf Douala Manga Bell da yai karatunsa a Jamus, yana son al'adar Jamusawa. Sai dai daga baya an ba shi kunya

02:37

This browser does not support the video element.

Saboda ya yi karatu a Jamus har zuwa jami'a, a farko ya yi kokarin amfani da fannin shari'a da ya koya a can. Lokacin da ya gano dabarun ba sa aiki, ya koma ga neman mutane su yi zanga-zanga a Douala. 

Yaya Rudolf Douala Manga Bell ya mutu? 

Jamusawa sun nemi kawar da tawaye lokacin da Yakin Duniya na Farko ya barke a 1914. Gwamnatin Jamus da ke mulki ta hukunta Rudolf Douala Manga Bell, wanda aka kama ranar bakwai ga watan Agusta na 1914, aka yanke masa hukuncin kisa saboda cin amana. 

A daren, Kanal Zimmermann ya ba shi dama, inda aka kwance masa sarkar da aka daure shi domin ya yi ban kwana da sarauniya da yerima. Rudolf Douala Manga Bell zai iya tserewa, amma ya dauki matakin dawowa washegari domin fuskantar mutuwa. Ranar takwas ga watan Agusta aka rataye sarkin na Douala. 

Kalamansa na karshe su ne: "Kuna rataye mutumin da ba shi da laifi. Kuna kashe ni ba tare da komai ba. Sakamakon zai zama gagarumi"

Yaya al'ummar Kamaru suke tunawa da Rudolf Douala Manga Bell?

Ana tuna shi a matsayin gwarzo wanda ya tashi ya tsaya a gaban Turawan mulkin mallaka. Wasu masana tarihi na daukar gwagwarmayar Marigayi Manga Bell a matsayin abin da ya sanya Kamaru ta samu 'yanci kai.

 

Wadanda suka taimaka da shawarwari wajen rubuta wannan tarihi sun hadar da Farfesan tarihi Doulaye Konaté da Dr. Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel  ce ta taimaka wajen kawo muku Tushen Afirka.