1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSpaniya

Rudun siyasa a Spain

Usman Shehu Usman
September 27, 2023

Siyasar kasar Spaniya ta kara shiga rudu bayan da Alberto Nunez Feijoo na jam'iyar People Party ya gaza samun nasarar zama firaminista a kuri'un da majalisar dokoki suka kada masa.

Treffen zur Regierungsbildung in Spanien
Hoto: Jesús Hellín/EUROPA PRESS/dpa/picture alliance

Alberto Nunez Feijoo wanda jam'iyarsa ta People Party ta samu rinjaye a zaben da ya gabata ya yi fatan zama firimiyan Spain, amma kuma a wannan larabar sai ya gaza samun kuri'u da yake bukata daga 'yan majalisar dokoki. Yanzu dai bisa dokokar kundin tsarin mulkin kasar  Spain, Feijoo na iya neman zama firaminista karo a na biyu a zauren majalisar dokonkin kasar, inda in ya samu karamin rinjaye hakan na iya ba shi damar darewar kujerar firimiyar kasar. Idan dai har a ranar Juma'a karo na biyu Feijoo bai samu nasara ba, to ya zama tilas wa Pedro Sanchez mai rikon kwaryan kujerar firaminista a yanzu, ya tattauna da jam'yar masu neman ballewa ta al'ummar Catalan domin samun kafa gwamnatin hadaka.