1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
IlimiAfirka

Rufe makarantu samakon tsoron garkuwa da yara

December 16, 2020

Jihohi biyar na arewacin Najeriya sun rufe makarantu bayan sace daliban sakandiren Kankara, lamarin da ke kara nuna matsalolin tsaro a yankin.

Nigeria Katsina | Kankara | Angriff auf Schule
Hoto: Abdullahi Inuwa/REUTERS

Rahotanni daga Arewacin Najeriya na cewar makarantu da dama a yankin za su rufe har zuwa wani lokaci bayan sace sama da dalibai 300 na makarantar sakandire da ke Kankara a jihar Katsina.

Yanzu haka akwai a kalla jihohi biyar da suka rufe makaranstun sun kuma umurci iyayen yaran da makarantun kwana da su kwashe yaransu, ciki hard a jihar Katsina da abin ya faru da jihar Zamfara da ke makwabtaka da ita sai jihar Kano da Jigawa da ma Kaduna.

Kwamishinan ilimi a jihar Zamfara Ibrahim Abdullahi ya ce suna da makarantu 10 ake cikin hatsarin wadannan maharan, ya ce hakan ya bar su da rashin zabi face su kulle makarantu.

Kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai ta dauki alhakin sace daliban na Kankara wanda dama ta ce karatun na boko haramun ne a Musulunci.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW