Rasha ta rufe ba wa Jamus makamshin gas
July 11, 2022Talla
Kamfanin da samar da isakar gaz din Rasha ne ya tabbatar da haka, inda yace katsewar za ta fara aiki daga wannan Litinin har zuwa tsawon kwanaki 10 masu zuwa, duba da muhimmancin aikin da zai yi wa bututan na Nord Stream 1 da suka ratsa tekun baltik.
Sai dai matakin na cigaba da haifar da fargaba a zukatan alummar Jamus da ke tsoron ko Rasha ka iya toshe hanyoyin samar wa Jamus din makamashin bayan kammala aikin, bisa dalilai na takon sakar diflomasiyya da ta barke tsakaninsu tun bayan soma mamayar Rasha a makwabciyarta Ukraine.
Gwamnatin Jamus ta kulla yarjejeniyar samar da makamashi da takwararta Jamhuriyar Chek a wani mataki na kandagarki.