1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ruftawar mahakar ma'adanai ta kashe mutane 101 a Kwango

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 16, 2025

Ko a cikin watan Yunin 2025 makamancin hadarin ya halaka mutane fiye da 200 a garin Rubaya na lardin arewacin Kivu.

Yadda ake hakar ma'adanan karkashin kasa a kudancin lardin Kivu na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Hoto: Alexis Huguet/AFP/Getty Images

Kimanin mutane sama da 100 sun halaka, sakamakon zaftarewar kasa a wajen hakar ma'adanan karkashin kasa ba bisa ka'ida ba a Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango, kamar yadda 'yan sanda suka sanar ranar Lahadi.

Sanarwar 'yan sandan ta ce ibtila'in ya faru ranar Juma'a a mahakar ma'adanai ta Mulondo Lwalaba, ta birnin Kolwezi na Lwalaba a kudancin kasar, wanda da farko aka yi hasashen cewa ma'aikata 70 kasar ta binne, to amma gawarwakin da aka zakulo zuwa safiyar Asabar sun kai 101, yayin da ake ci gaba da laluben sauran da ba gani ba.

Karin bayani:Harin ta'addanci ya kashe mutanen Jamhuriyar Kwango kusan 20

Ko a cikin watan Yunin 2025, makamancin hadarin ya janyo asarar rayukan masu hakar ma'adanai fiye da 200 a gabashin garin Rubaya na lardin arewacin Kivu.