Ruguntsumin siyasar Pakistan
October 4, 2007Jamiár tsohuwar P/M Pakistan Benezir Bhutto ta ce mai yiwuwa ne ta janye daga zaɓen da majalisar dokoki zata yi na shugaban ƙasa wanda ka iya kawo cikas ga burin Shugaba Pervez Musharraf na yin tazarce. A yau jamíyar za ta gudanar da babban taro a London domin yanke hukunci ko zata bi sahun yan majalisar dokoki 85 wanɗanda suka yi murabus domin adawa da tsayawar Musharraf. Benezir Bhutto ta shaidawa manema labarai cewa akwai yiwuwar jamíyar su ta PPP ka iya janyewa daga zaɓen sakamakon abin da ta ce an kasa cimma daidaito a shawarwarin rabon madafan iko tsakanin ta da Musharraf da kuma batun maido da mulkin dimokradiya a Pakistan. Musharraf wanda ya ɗare ragamar mulkin ƙasar Pakistan bayan juyin mulki a shekarar 1999 wanda kuma a yanzu ya kasance babban aminin ƙasar Amurka yana fatan lashe zaɓen kasancewar waɗanda yake ƙawance da su, sune suka fi rinjaye a majalisun tarayya dana gundumomi waɗanda za su kaɗa ƙuriár. Yace yan majalisa 163 ne kacal suka yi murabus daga cikin adadin yan majalisar 1,170