1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rukuni na biyu na 'yan sandan Kenya na shirin zuwa Haiti

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 3, 2024

Hare-haren 'yan daban Haiti ya tilasta wa firaminista Ariel Henry yin murabus a cikin watan Mayun da ya gabata

Hoto: REBECCA NDUKU/PRESIDENTIAL COMMUNICATION SERVICE/EPA

Rukuni na biyu na 'yan sandan Kenya zai isa kasar Haiti nan da 'yan makonni, domin aikin wanzar da zaman lafiya a kasar da ke fama da 'yan daba masu rike da makamai, kamar yadda firaministan Haiti Garry Conille ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Karin bayani:Lauyoyi a Kenya na yunkurin dakile shirin tura 'yan sanda zuwa Haiti

Mr Conille wanda yanzu haka ke ziyara a Washington inda ya gana da ministan harkokin wajen Amurka Antony Blinken a fadar White House, ya ce isar ayarin 'yan sandan Kenya zuwa Haiti zai taimaka wajen kara wanzar da lafiya a kasar, wadda ta yi fama da boren 'yan daba da suka kwace iko da Port-au-Prince babban birnin kasar a cikin watan Fabarairun da ya gabata, a kokarinsu na hambarar da firaminista Ariel Henry.

Karin bayani:'Yan Kenya na adawa da matakin gwamnatin na tura 'yan sanda a Haiti

Hare-haren 'yan dabar ya tilastawa firaminista Ariel Henry yin murabus a cikin watan Mayun da ya gabata, daga nan ne ma tawagar farko ta 'yan sandan Kenya su 200 ta sauka a kasar a cikin watan Yunin da ya gabata, domin aikin wanzar da zaman lafiya bisa kulawar Majalisar Dinkin Duniya.

An dai zargi 'yan tarzomar da kisan fararen hula da yi wa mata fyade da yin garkuwa da mutane, baya ga sace-sace da kuma janyo cikas ga aikin samar da agaji ga mabukata da suka halin tagayyara a Haiti.