Rundunar G5 Sahel na fuskantar tarin matsaloli
November 3, 2017Baya ga kudaden tafiyar da aikin da sabuwar runduna ta G5 Sahel ta kasa samu, akwai kuma batun irin ayyukan da ya kamata ta yi da ba a kayyade ba. A watan Maris na 2018 ne wannan runduna ya kamata ta soma aikinta gadan-gadan da sojojinta 5000, wadanda za a rarraba cikin bataliyoyi bakwai. Jamhuriyar Nijar da Mali ne ya kamata su bada bataliyoyi biyu biyu, yayin da sauran kasashen na Chadi, Burkina Faso da Moritaniya za su bada daya kowaccensu. Cibiyarsu ta aiki G5 Sahel za ta kasance a birnin Sevare da ke tsakiyar kasar Mali.
Mamane Seidou, kusa a cikin tsari na G5 Sahel a bangaren Jamhiriyar Nijar ya ce: "Akwai yanki na Gabas wanda ya shafi iyakar Nijar da Chadi, akwai yanki na tsakiya wanda ya shafi kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, sannan akwai yanki na Yamma wanda shi kuma ya shafi iyakatr Mali da Moritaniya. wannan shi ne tsarin da aka yi inda za a zuba wadannan sojoji, kuma dukannin kasashen za su yi kokarin ganin sojojinsu sun bi wannan tsari."
Sai dai kuma bangarori da dama na nuna shakku kan karfin wannan runduna ta G5 Sahel wajen iya tafiyar da wannan aiki. A cewar Issa N'Diaye tsohon minista na kasar Mali, kuma shugaban kungiyar tattaunawa tsakanin al'ummar kasar Mali, warware matsalar mayakan jihadi ba wai batu ne kawai na soja ba.
Ya ce "Tarihi ya nunar de cewa, tun daga kasar Afghanistan, da ma sauran wuraren da ake yaki da 'yan jihadin batun nuna karfin soja ba ita ce hanya mafi dacewa ba. Abin da ya kyautu shi ne na neman sanin dalillan wannan matsala tun daga tushe, musamman ma neman gano ina ne 'yan jihadin ke samun kudadensu."
Kasafin kudin ayyukan wannan runduna ya tashi a miliyan 423 na Euro a shekara. Sai dai kasar Faransa ta bayar da shawarar ganin an dawo da wannan adadi kasa ya zuwa miliyan 250 na Euro. A yanzu dai ana iya cewa akwai tabbacin samun miliyan 100 na Euro idan aka duba alkawuran da Tarayyar Turai da Amirka suka yi na bada nasu tallafi ga wannan runduna, kuma suma kasashen biyar na G5 sahel ta yi alkawarin bada miliyan 10 na Euro kowaccensu. Sannan kasar Faransa za ta bayar da miliyan takwas na Euro.