Janar Haftar ya bar Mosko ba tare da yarjejeniya ba
January 14, 2020A jawabin da ya gabatar kai tsaye ta gidan Telebijin din kasar, jim kadan bayan da janar Khalifa Haftar ya sa kafa ya yi fatali da batun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wutar, ya kuma fice ya bar kasar Rasha da ta shirya taron, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ke mara baya ga gwamnatin Faeez Sarraj mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ba za su lamunta da ci gaban salwantar rayukan dubban mutane a kasar Libiya ba.
"Lokacin da za a wa al'ummar Libiya adalci ya yi. Ba za mu lamunta da wani dan tawaye mai yunkurin juyin mulki ya ci gaba da yin kasada da rayukan 'yan Libiya ba. Wannnan batu ne da ya zama wajibi mu tattauna kansa a yayin taron da zai gudana a birin Berlin na Jamus, wanda wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afrika baya ga kasashen Larabawa za su halarta."
Khalifa Haftar dai ya fice daga dakin taron na Mosko ya ma bar kasar ta Rasha, ya yi watsi da bukatun da yarjejeniyar zaman lafiyar ta kunsa. Ko da dai Rashan wadda ke matsayin aminiya ga Haftar ta sha alwashin shawo kan matsalar. Yadda a wani taron manema labarai, ministan harkokin wajenta Sergei Lavrov ya ce Rasha za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin Khalifa Haftar ya amince da yarjejeniyar.
To sai dai kamar yadda wani na hanun damar janar Haftar, Idris Imad Warfally ke cewa, babu ta yadda za su lamunta da yarjejeniyar da ke kokarin ba wa 'yan ta'adda kariya a Libiya.
"Wannan yarjejeniyar wani yunkuri ne na ceton gwamnatin Sarraj da ke ba wa 'yan ta'adda kariya. Babu ta yadda za mu lamunta da janyewa daga birnin Tripoli. Ba za kuma mu lamunta da sanya sojojin Turkiyya cikin masu sanya ido ga wannan tsagaita wutar ba, domin su sojojin mamaya ne. Idan kuma har da gaske ana son tsagaita wuta, to a kwashe 'yan ta'addar da Turkiyya ta shigo da su Libiya a mayar da su can yankinsu na Idlib na Siriya da sauransu."
Da ma tun a safiyar wannan Talata kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto shafin Facebook na sojojin Haftar na fadin cewa a shirye suke su kwace birnin Tripoli da karfi.
A nasa bangaren, shugaban gwamnatin hadakar ta Libiya, Faeez Sarraj, wanda ya rattaba hannu kan yarjejeniyar, ya ce a shirye yake a zauna lafiya a kasar, amma bisa sharuddan dole ne Haftar ya janye daga yankuna da ya mamaye a baya-bayan nan.
Wannan duk dai na wakana ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke tattauna yiwuwar tura dakarun shiga tsakani don tabbatar da tsagaita wuta a Libiya, don kuma samun kwakkwarar madogara ga taron sulhun da ake shirin gudanarwa a birnin Berlin na Jamus a mako mai zuwa.