Majalisar Dinkin Duniya ta nada sabon shugaban MINUSCA
August 14, 2015Sabon shugaban rundunar ta MINUSCA Parfait Onanga-Anyanga dan kasar Gabon ya maye gurbin tsohon shugabanta Babacar Gaye dan asalin kasar Senegal. Wanda majalisar ta kora bayan da aka zargi dakarun rundunar, da aikata miyagun laifuka da suka hadar da cin zarafin kananan yara ta hanyar yi musu fyade. Zargi na baya-bayan nan dai shine wanda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi a makon da ya gabata wanda wata yarinya mai kimanin shekaru 12 ta shaidar da cewa daya daga cikin dakarun rundunar ta MINUSCA ya yi mata fyade yayin wani bincike da dakarun suka gudanar a gundumar PK5 da ke zama wajen da Musulmin kasar ke da zama. Kafin nadin Onanga-Anyanga a matsayin sabon jagoran rundunar ta MINUSCA a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai, shine jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Burundi.