SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya za su bar Kwango
November 22, 2023Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da matakin a wata sanarwar da ta fitar a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, sai dai a cikin sanarwar ba a yi wani karin haske kan jadawalin ficewar ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.
Tun a shekarar 1999 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta girke rundunar tsaro da kwanciyar hankali ta Monusco a Kwangon, wacce ke kumshe da dakaru dubu 14 galibi a yankin gabashin kasar.
Yawaitar hare-haren 'yan bundiga da kazancewar al'amurra, sun sa gwamnatin Kwangon ta bukaci da a janye dakurun cikin hanzari a gabanin sake wa rundunar sabon wa'adi.