1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za mu ceto 'yan matan Chibok- Buhari

Ubale Musa/ MNAJuly 8, 2015

A ganawar da ya yi da masu fafutukar ceto 'yan matan Chibok, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya amsa cewa sojojin kasar sun gaza wajen tabbatar da ceto 'yan matan.

Buhari BBOGs
Hoto: Getty Images/Afp/P. Ojisua

A wani abun da ke zaman alamun sauyi a cikin yaki da ta'addancin a Tarrayar Najeriya, a gaban manyan hafsoshin tsaro shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da gazawar sojan wajen tabbatar da ceto yaran da suka share sama da shekara guda a dokar daji.

'Ya'yan kungiyar da ke fafutukar kwato 'yan mata 'yan makaranta na Chibok sun rera taken al'adarsu a fadar shugaban kasar bayan kammala ganawa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karon farko.

A baya dai 'ya'yan kungiyar sun sha ji a jiki a hannu na tsohuwa ta gwamnati da jami'an tsaro da ke musu kallon laifi a cikin fafutukar ceto yaran da aka sace a watan Aprilun shekarar 2014.

Kokarin kwantar da hankalin iyayen yara

Oby Ezekwesili ta kungiyar BBOGs lokacin jawabinta a ganawa da Shugaba Buhari a AbujaHoto: Getty Images/Afp/P. Ojisua

Duk da cewar dai gwamnatin kasar ta gaza wajen neman afuwar gazawa ta jami'an tsaron ta wajen satar yaran dai, damar tozali da shugaban kasar da ma kalamai na kwantar da hankali daga dukkan alamu sun kwantar da hankali kama daga iyayen yaran ya zuwa 'yan fafutukar da suka yi tururuwa suka kuma fadi iya son ransu ga gwamnatin.

Mrs Maryam Uwais dai na zaman jagorar kungiyar da ta karanta jawabi dogo da nufin jaddada matsayinsu na fafutuka don tabbatar da ceto yaran, kuma a fadarta a karon farko ta hango haske a kokari na ceto yaran da kila ya kai karshen matsalar a cikin sauri.

To sai dai koma ya zuwa yaushe ne dai keyar yaran ke iya baiyana a ga 'yan uwa da abokai dai wannan rana ta Laraba na zaman ta 450 a hannun 'yan kungiyar Boko Haram da a tunanin Dr. Emman Shehu daya a cikin masu ziyarar ke zaman garkuwa ta karshen-karshe a hannu na kungiyar ta masu ta da zaune tsaye da ke dada nuna alamar fuskantar matsatsi yanzu.

To sai dai koma ya zuwa yaushe amfanin 'yan matan ke iya kaiwa karshe dai an dauki lokaci ana rade-radin yiwuwar amfani da wasunsu wajen kuna ta bakin waken da ke kara yawa a sassa daban-daban cikin arewacin kasar da ma na makwabta yanzu.

Hauwa Abubakar (a hagu) wadda ta wakilci 'yan matan makarantar Chibok, a ganawa da Shugaba BuhariHoto: Getty Images/Afp/P. Ojisua

Tunanin kuma da bai zo dai-dai da hasashen Reverend Inoch Mark da ke zaman daya a cikin iyayen yaran ba.

Samar wa jami'an tsaro isassun kayan aiki

Babban taimako a bangaren na gwamnatin dai na zaman inganta jami'an tsaro da kayan aiki da nufin cika burin da a baya ke zaman wasan yara ga kasar a fadar shugaban kasar da ya ce ta yi baki ta baci a harkar soja.

"Abun mamaki ne a ce abun da sojan Najeriya suka cimma daga Burma zuwa Zayya da Liberiya da Saliyo da Kudancin Sudan, a ce wai yanzu sai kasashe irinsu Nijar da Chadi da Kamaru sun tallafi Najeriya. Ga yadda manya suka fadi. Za mu yi iyaka na kokari don sake farfado da kimar kasarmu da cibiyoyi na tsaron ta. Kuma da dagewarku za mu kyale ku yin duk abun da kuke iyawa, kuma za mu yi nazarin shawarwarinku.”

Sabuwar ganawar dai na zaman alamar sauyi a banagren kasar da jami'ai tsaronta da kusan dukkaninsu suka kasa kunne don jin suka ta kungiyar da ma iyayen yara, a cikin yakin da a baya ya kalli nisan banbanci a tsakanin jami'an tsaro da 'yan kasar da ke neman sauyi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani