1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar sojan Masar a tsaka-mai-wuya

January 31, 2011

A daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zanga a Masar, shin wace irin rawa sojojin ƙasar za su taka tattare da halin da ƙasar take ciki da kuma makomar Shugaba Hosni Mubarak?

Kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a MasarHoto: AP

Tsohon shugaban rundunar mayakƙn sama ta Masar, kuma babban kwamandan askarawan ƙasar a yanzu, Hosni Mubarak tsawon shekaru 30 kenan yaka mulki ƙarƙashin dokar-ta-ɓaci. Har ya zuwa tashin hankalin na yanzu, sojoji dai sun zama manyan masu goyon bayan mulkin na Mubarak. To amma girman zanga-zangar da fushin da jama'a suke nunawa sun sanya ala tilas Mubarak ya rushe gwamnatin da al'amura da alamu suka fi ƙarfinta, ya kuma naɗa manyan makusantansa ga muƙamai masu muhimanci. Ranar Asabar ya naɗa shugaban hukumar leƙen asiri Omar Suleiman kan muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, sa'annan ministan suhurin jiragen sama, kuma tsohon kwamandan rundunar jiragen saman Masar, Ahmed Shafik a matsayin sabon shugaban gwamnati. Dukkansu suna da tarihin taka muhimmiyar rawa a aiyukan rundunar ta Masar, abin da ake iya cewar yanzu dai lokacin da sojojin Masar suma za'a dama da su a harkokin mulkin ƙasar yazo.

Duk da haka, abin tambaya shine: wace irin rawar rundunar sojan za ta taka a gwagwarmayar neman madafun iko a Masar. Akwai raɗe-raɗi da jita-jita game da haka, inda ma ake cewar wai angizo mafi tsanani ga sojojin na Masar yana zuwa ne daga Washington. Shin ko sojojin za su ci gaba da nuna biyayya ga Shugaba Mubarak da ke ƙara shiga cikin wani hali na tsaka-mai-wuya a ƙasarsa? Tsohon Janar na sojan ƙasar, kuma masani kan al'amuran tsaro a Alƙahira, Talat Musallam ya ce bashi da wannan ra'ayi, saboda yana ganin rundunar sojan a matsayin runduna ce ta kare kasa, amma ba ta kare mulkin wani mutum ba.

"Aikin da ke kan rundunar sojan Masar da farko shi ne ta tabbatar da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma ba ta goyi bayan mulkin wani ɗan siyasa ba. Abubuwan da ke gudana a yanzu, sun nunar a fili cewar sojojin ba sa bin umurnin shugabanninsu sau da ƙafa. Hakan shi ya sanya ba na zaton za su zama masu goyon bayan Hosni Mubarak".

Ci gaba da zanga-zangar adawa da shugaba MubarakHoto: AP

A yanzu haka ma, sojojin tuni sun dakace muhimman gine-gine na gwamnati a birnin Alƙahira, kamar tashar Television ta hukuma da ke bakin kogin Nil da babban gidan ajiye kayan tarihi da fadar shugaban ƙasa. Shugabannin sojan suna ƙoƙarin ganin ƙasar ta Masar ba ta faɗa cikin halin ruɗani gaba ɗaya ba, bayan da rundunar 'yan sanda tun daga kwanakin baya ta kasa samun nasarar tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ranar Lahadi aka kuma tura sojojin su tabbatar da tsaro a cibiyar 'yan yawon shaƙatawa da ke Sharm-el-Sheikh a gaɓar tekun Bahar-Maliya.

A daura da rundunar 'yan sandan Masar da tayi ƙaurin suna saboda cin rashawa, sojojin Masar har yanzu suna da mutuncinsu tsakanin al'ummar Masar. Sojojin ma sun baiyana marhabin da mafi yawan halin da ake ciki na zanga-zanga, inda ma aka riƙa ganin alamu na zumunci tsakanin sojojin da matasa 'yan zanga-zanga, waɗanda a fili suke iya yin jawabai da ke zama cin mutunci ga Shugaba Mubarak.

Masana al'amuran siyasa gaba ɗaya sun daidaita a kan cewar sojojin suna da cikakken ƙarfin da za su iya zama wuƙa da nama ga makomar Shugaba Mubarak. Masanan suka ce suna ma iya hangen yiwuwar kafa gwamnatin wucin gadi ƙarƙashin shugabancin janarorin ƙasar, ko da shi ke yana da wuya a hangi irin matakin da sojojin za su ɗauka da kuma yawan angizon da Mubarak yake da shi tsakanin rundunar ta soja. Tsohon Janar Talat Musallam yace:

"Yana da wuya a hangi irin matakin da shugabannin sojan za su yanke ƙudirin ɗauka, musmaman ganin cewar ministan tsaro, Hussein Tantawi har yanzu bai fito da ra'ayinsa ba tukuna. Har yanzu bamu kuma san yadda dangantaka take tsakaninsa da sShugaba Mubarak ba."

Mawallafi. Loay Mudhoon/Umaru Aliyu
Edita: Halima Balaraba Abbas

Za ku iya sauraron rahoton a ƙasa.