Rundunar sojin Jamus ta janye rabin dakarunta da ke Mali
November 10, 2023![](https://static.dw.com/image/60562039_800.webp)
Rundunar sojin Jamus ta ce fiye da rabin sojojinta da ke cikin dakarun wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali sun bar kasar, inda ta bar guda 50 kadai a kasar, sai kuma guda 100 da ke Jamhuriyar Nijar har yanzu.
Karin bayani:Jaridun Jamus: Dakatar da zabe a Mali
Mai magana da yawun rundunar ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Jamus DPA cewa sun tsara kammala janye sojojinsu baki-daya daga kasar ta Mali daga nan zuwa karshen shekarar nan da muke ciki.
Karin bayani:Agajin Jamus a wasu kasashen Afirka ta Yamma
A cikin watan Yunin da ya gabata ne dai sojojin da ke mulki a Malin ne suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta janye dukkan sojojinta dubu goma sha biyu da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, bayan da ta fara dasawa da Rasha sakamakon kulla kawancen tsaro.