1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojin Najeriya sun kammala rahoton kisan mutanen Tudun Biri

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 20, 2024

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya ba da umarnin gudanar da binciken don gano musabbabin abin da ya faru

Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Rundunar sojin Najeriya ta ce a karshen watan nan Fabarairu za ta fitar da rahoton yadda jiragenta marasa matuka suka kashe mutane 85 a kauyen Tudun Biri na jihar Kaduna bisa kuskure a cikin watan Nuwamban bara, lokacin da suke tsaka da taron maulidi.

Karin bayani:An binne gawa 85 a kauyen Tudun Biri

Babban hafsan tsaron kasar Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Talatar nan a Abuja babban birnin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito, yana mai jaddada cewa aikinsu shi ne kare rayukan al'umma amma ba wai kai musu hari ba.

Karin bayani:Ana jimamin mutuwar shugaban sojin Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya ba da umarnin gudanar da binciken don gano musabbabin abin da ya faru.