1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

India ta kwato jirgin Iran daga hannun 'yan fashin teku

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 29, 2024

'Yan fashin tekun Somalia sun kama jirgin kasar Sri Lanka, kamar yadda rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta sanar. To amma a Litinin din nan ne Seychelles ta sanar da kubutar da jirgin da mutanen cikinsa.

Hoto: Indian Navy /AP/picture alliance

Rundunar sojin ruwan India ta sanar da kubutar da jirgin kamun kifin kasar Iran da 'yan fashin teku suka kama a ruwan Somalia, bayan harin da aka kai masa a kogin Baharmaliya.

karin bayani:Harin Houthi ya dakatar da aikin kamfanin Jamus

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Vivek Madhwal ya fitar ta ce su ma mutanen cikin jirgin su 17 an samu nasarar kubutar da su lafiya.

Karin bayani:Yaki da 'yan fashi teku a mashigin Guinea

Ko a ranar Asabar din da ta gabata ma 'yan fashin teku daga Somalia sun kama jirgin kamun kifin kasar Sri Lanka da mutane 4 da ke cikinsa, kamar yadda rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta sanar. To amma a Litinin din nan ne fadar shugaban kasar Seychelles ta sanar da kubutar da jirgin da mutanen cikinsa.