1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojin saman Najeriya sun kashe gomman 'yan ta'adda

August 24, 2025

An halaka 'yan ta'addar kusan 40 a yayin wasu hare-hare da rundunar sojin sama ta kai a wasu wuraren haduwar mayakan a iyakar Najeriya da Kamaru.

Jahrestag der nigerianischen Luftwaffe
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da halaka 'yan ta'adda fiye da 35 a wani samame da ta kaddamar a jiya Asabar a kan mayakan masu ikirarin jihadi a lokacin da suke taro a kusa da iyakar kasar da Kamaru.

A sanarwar da rundunar ta fitar ta ce ta yi amfani da bayanan sirri da ta samu dangane da wasu wurare daban-daban har guda hudu inda 'yan ta'addar ke taruwa kafin ta kai jerin hare-hare ta sama, inda ta samu nasarar fatattakar su tare da halaka mayaka fiye da 35.

Karin bayani: Nasarar yaki da ta'addanci a Najeriya  

Rundunar sojin saman ta Najeriya ta kuma kara da cewa ta zage damtse tare da matsa kaimi a fagen daga domin hana wa 'yan ta'adda sukuni musamman samun damar kai hare-hare.

Hakazalika rundunar ta ba da tabbacin cewa wannan samame da ta kai na nuni da irin sabuwar damarar da ta yi domin bai wa rundunar sojin kasa tallafi ta sama, domin dakile hanyoyin da 'yan ta'adda ke bi a yankunan kan iyaka na arewa maso gabashin Najeriya.