1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iNajeriya

Najeriya: Rusau sakamakon ambaliya

July 17, 2024

Ambaliyan ruwa ta rusa daruruwan gidaje da gonaki tare da raba dubban mutane da matsugunansu a kauyukan Mainok da Jakana da ke jihar Bornon Najeriya, tare da jefa al'umma cikin mawuyacin hali.

Najeriya | Ambaliyar Ruwa | Borno | Barna
Ambaliyar ruwa ta yi barna a jihar Bornon NajeriyaHoto: Muhammad Bello Ibrahim/DW

Sai dai hukumomi a jihar ta Borno sun dauki matakai na gagawa, domin sake tsugunar da wadanda ambaliyar ta shafa tare da ba su agajin gaggawa kafin daukar matakai na din-din-din. Bayan kwashe kwanani biyu ana ruwan sama ba kakkautawa ne ruwa ya ballo ta bangarori da dama a kauyen Mainok da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno, wanda ya lalata gidaje da gonakin al'umma. Yayin da wasu ke alakanta wannan ambaliyar ruwa da ballewar wasu Koguna da ke kusa da garin, wasu kuma na cewa yawan ruwan sama da aka yini ana yi ne da kuma rashin magudanan ruwa suka janyo ya shiga cikin gidajen mutane da gonaki. Al'ummar da ke zaune a gidajen da ambaliyar ta shafa sun yi cirko-cirko a bakin hanya ba tare da sanin ina za su ba, inda wasu ke ta kokarin kwaso 'yan kayayyakinsu da abin da ya saura a gidajen wadanda yawancin na kasa ne.

Matsalar ambaliyar ruwa a Najeriya

02:18

This browser does not support the video element.

Yanayin da suke ciki abun tausayawa ne, saboda dan kayan abincinsu ma ruwan ya lalata ko kuma kasa ta rufta a kai ko ruwan da za su sha ma wahala yake musu saboda gurbacewar da ya yi.  Ambaliyar ruwan ta kuma yanke babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu mai matukar muhimmanci da ta hada jihar Borno da sauran sassan Najeriyar, inda matafiya suka samu tsaiko. Wani matafiyi Muhammad Nazir ya ce, sun shafe tsawon lokaci suna jiar hanyar da za su wuce. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Borno da ta tabbatar da irin barnar da ambaliyar ta yi da ma wuraren da ta shafa, ta ce tana daukar matakai na tallafa wa  wadana ta yi wa ta'adin. Babban daraktan hukumar Dakta Barkindo Muhammad Sa'idu ya ce, ba kawai Mainok wannan ambaliyar ruwan ta sahfa a jihar ta Borno ba. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi a Najeriyar ke kara yin gargadin samun ambaliya a jihohin Borno da Yobe da wasu jihohin kasar 20, abin da ya sa masu rajin kare muhalli ke kara jan hankulan gwamnatoci su dauki matakai na magance matsalar ko rage barnar da za ta yi.