1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rushewan Gini a Masar

Zainab MohammedDecember 24, 2007

Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a sakamakon rushewan wani ginin bene mai hawa 12,a birnin Alexandria dake arewacin kasar Masar.Wani jami’an gwamnatin kasar daya ki a ambaci sunan sa yace ,har yanzu akwai mazauna gidan dake makale a karkashin rusasshen ginin benen.Jamian ‚yansanda sun sanar dacewar ginin wanda akayi shi kimanin shekaru 30 tun asali nada hawa bakwai ne,kafin a yan shekarun da suka gabata aka dora hawa biyar,wanda ya mayar dashi hawa 12.A masar din dai ana cigaba gine gine ba bisa tsari da kaidojin gwamnati ba.