1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rushewar gini a Abuja ya yi sanadin rayukan mutane

Binta Aliyu Zurmi
August 26, 2022

Wani ginin bene mai hawa uku da ake aikin ginisa ya rufta a unguwar Kubwa da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

China | Einsturz eines Gebäudes in Changsha
Hoto: Chen Zeguo/AP Photo/picture alliance

 

Faduwar ginin dai ya rutsa da mutanen bakwai a ciki inda jami’an biyu daga cikinsu suka mutu yayin da jami’an hukumar kai daukin gaggawa ta Abuja suka samu ceto mutane biyar daga baraguzan ginin.

Ginin da aka  tsara shi a yanayi na kasuwar zamani da ke da shaguna, ya fadi ne a yayin da ake sanya masa daben zamani watau gab da kamala aikinsa ke nan.

Ya zuwa yanzu ba akai ga sani dalilin faduwar wannan ginin ba. Ana yawan samun faduwar gini a Najeriya, musamman a yankin kudancin kasar.