1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ruto ya rusa majalisar ministocinsa

July 11, 2024

Wannan shi ne babban mataki da shugaba William Ruto ya dauka tun bayan zanga-zangar karin haraji da ta nemi kifar da gwamnatinsa.

Shugaban kasar Kenya William Ruto
Shugaban kasar Kenya William RutoHoto: TONY KARUMBA/AFP

Shugaban Kenya William Ruto ya rusa kusan dukkan mambobin majalisar zartarwarsa tare da shirin kafa wata mai mutane kalilan.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da  Mr. Ruto ke fadi tashin farfado da kimarsa bayan zanga-zangar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane a kasar.

Kasar ta gabashin Afrika ta fuskanci zanga-zanga mai zafi kan karin kudin haraji, lamarin da ya koma tarzoma da neman kifar da gwamnati bayan masu zanga-zangar sun yi arangama da jami'an tsaro da kuma kutsawa majalisar dokokin kasar.

Kenya: Masu bore sun sake fitowa a Nairobi

Kadan da suka sha daga jijjigar da Ruto ya yi wa gwamnatinsa sun hada da ministan harkokin waje Musalia Mudavadi da mataimakin shugaban kasa Rigathi Gachagua.