Ruwa ya yi barna a sansanin yan gudun hijira
June 4, 2017Majalisar Dinkin Duniya ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da guguwa da aka yi a karshen mako nan a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun yi munmunar barna a matsugunnan 'yan gudun hijira wadanda yakin Boko Haram ya raba da gidajensu a cikin jihar Borno, inda har mutun daya ya ransa ransa a sansanin 'yan gudun hijira na Bakasi a Maiduguri.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar wato OIM wacce ta sanar da hakan a wannan Lahadi ta ce mutane akalla dubu 4,300 ne matsalar ta shafa musamman a matsugunnin 'yan gudun hijira na Jere da Kaga da Konduga da Maiduguri.
Hukumar ta OIM ta ce babban aikin da ta sa gaba a halin yanzu shi ne na gyara wuraren kwanciyar 'yan gudun hijirar da gina magudanan ruwa da kuma samar da ingantattun gine-gine wadanda 'yan gudun hijirar za su dinga fakewa a duk lokacin da hadari ya taso.