Ruwan sama sun kashe mutane 78 a China
June 23, 2016Talla
Kamfanin dillancin labaran kasar ta China ya ruwaito cewar ruwan saman ya kuma tafi da gidaje da dama a birnin Yancheng. Yankunan kasar ta China da dama ne dai suka fuskanci ruwan sama mai tsananin gaske a wannan mako.
Abin da ya haddasa asarar rayuka da dama, da ta kadarori da aka kiyasta darajarsu a miliyan 410 na Dalar Amirka, a yayin da mutane dubu 200 suka rasa muhallansu.