1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin wadanda suka mutu a Brazil ya karu

Abdourahamane Hassane
May 31, 2022

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haddasa ambaliya da zabtarewar kasa a kusa da Recife da ke arewa maso gabashin Brazil, ya kashe mutane akalla 100, a cewar wani sabon rahoto da hukumomin yankin suka bayar.

Brasilien Flut Amazonas Careiro Da Varzea
Hoto: Bruno Kelly/REUTERS

Gwamnatin Jihar Pernambuco, wadda Recife ce babban birninta, ta bayar da rahoton bacewar mutane 14, yayin da ake ci gaba da bincike a yankunan da lamarin ya fi shafa domin gano ko akwai masu sauran shan ruwa a gaba. Kwararru a kan sha'anin kare muhali sun ce dummamar yanayi  da rikedewar dazuzzuka zuwa birane na daga cikin dalilan da suka janyo saukar ruwan sama da ya wuce kima.