Miliyoyin 'yan Ruwanda ne, suka yi rejistar kada kuri'a da nufin zaben sabon shugaban kasa tare da sabunta kujerun 'yan majalisar dokokin kasar.
Talla
To amma mene ne sakamakon wannan zaben zai iya haifar wa a fagen siyasar Ruwanda? kuma ya dangantakarta da ta tabarbare da kasashe da dama na duniya za ta kasance, yayin da Ruwandaa ta samu zaman lafiya da ci-gaban tattalin arziki? Shekaru 30 bayan kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi a Ruwanda, kasar ta farfado har ma ta fara tsayawa da kafafunta. Kama daga fannin ingantacciyar rayuwa, har zuwa ga ci-gaban tattalin arziki da more rayuwa da kuma zuba jari na kasashen waje. Masana sun nunar da cewa, Ruwanda ta samu ci-gaba sosai a fannin samar da ababen more rayuwa ko gidaje da aka lalata a lokacin kisan kare dangi. Duk ma da rashin daidaito da ake ci-gaba da samu a tsakanin al'umma da kuma rashin bai wa yankunan karkara da akasarin al'ummar kasar ke rayuwa fifiko, ammam tsarin sake gina tattalin arzikin kasar Ruwanda ya kasance babbar nasara da ba za a iya musantawa ba. Sai dai akwai wani bangare mai muhimmanci da ake ci gaba da sukar kasar da Paul Kagame ke shugabanta a kai, wanda ba wani ba ne illa na kare hakkin dan Adam. Amma Hassan Kannenje da ke zama daraktan Cibiyar Horn da ke nazarin dabarun siyaya na kasa da kasa, ya ce Ruwanda ta yi la'akari da yakin da ta yi fama da shi wajen fuskantar wannan alkibla.
Kwanaki 100 na kisan kare dangi a Ruwanda
Har yau kisan kare dangi da aka yi a Ruwanda shekaru 25 da suka wuce, yana daukar hankalin duniya. A 1994 gamaiyar kasa da kasa musamman Majalisar Dinkin Duniya da kasar Faransa sun juya wa al'ummar Ruwanda baya.
Hoto: Timothy Kisambira
Alamun tsattsauran ra'ayi
Ranar 6 ga watan Afrilun 1994 wadanda ba a sani ba suka kakkabo jirgin saman da ke dauke da shugaban Ruwanda Juvenal Habyarimana lokacin da yake kokarin sauka a filin saukar jiragen saman birnin Kigali. Shugaba Habyarimana da takwaransa na Burundi sun mutu a harin. Kwana guda bayan haka aka fara kisan da aka tsara. An ci gaba da kisan kare dangin inda cikin watanni uku aka hallaka mutane 800,000.
Hoto: AP
Kisa da nufi
Bayan hallaka shugaban, 'yan Hutu masu matsanancin ra'ayi sun kai hari kan tsirarun 'yan Tutsi da Hutu masu sassaucin ra'ayi. Wannan kisa ne da aka shirya a kan 'yan fafutuka, da 'yan jarida da 'yan siyasa. Daya daga cikin wadanda aka fara kashewa ranar 7 ga watan Afrilu ita ce Firaminista Agathe Uwiringiymana.
Hoto: picture-alliance/dpa
Ceto 'yan kasashen ketare
Ana kashe dubban 'yan Ruwanda kowace rana, sojoji musamman na Beljiyam da Faransa sun kwashe 'yan kasashe ketare kimanin 3,500. Ranar 13 ga watan Afrilu sojojin Beljiyam sun ceci ma'aikata bakwai Jamusawa da ke aiki da tashar Deutsche Welle mai yada shiri daga Kigali. Ma'aikata 'yan kasar Ruwanda 80 kacal daga cikin 120 ne suka tsira daga kisan kare dangin.
Hoto: P.Guyot/AFP/GettyImages
Kira kan neman taimako
A farkon watan Janairun 1994 shugaban dakarun kiyaye zaman lafiya Romeo Dallaire ya nemi daukar mataki kan labarin da ya samu na shirin hallaka 'yan Tutsi. Amma sakon gargadin da ya tura wa Majalisar Dinkin Duniya ranar 11 ga watan Janairu an yi biris da shi. Kofi Annan karamin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da tsari ya yi watsi da maganar yuwuwar kisan kare dangin.
Hoto: A.Joe/AFP/GettyImages
Sakonnin tsana na kafofin yada labarai
Gidan rediyon RTLM da Kangura da wata mujalla mai fitowa mako-mako cike suke da sakonnin tsana na kabilanci. A shekarar 1990, Kangura ta buga wasu ka'idoji 10 na Hutu, rediyon RTLM ya yi suna wajen kade-kade da labarin wasanni, da kuma ziga 'yan Hutu su hallaka 'yan Tutsi marasa rinjaye. Daraktanta Milo Rau ya sadaukar da kai wajen tsara fim na "Tsanan Rediyo"
Hoto: IIPM/Daniel Seiffert
'Yan gudun hijira a otel
A birnin Kigali, Paul Rusesabagina ya boye fiye da mutane 1,000 a otel mai suna "Hotel des Milles Collines". Rusesabagina ke zama manajan otel din na dan kasar Beljiyam wanda ya bar kasar. Sakamakon amfani da kudi da giya, ya taimaka wajen kare 'yan Hutu masu matsanancin ra'ayi daga kisan 'yan gudun hijira. A wurare masu yawa 'yan gudun hijira ba su tsira ba.
Hoto: Gianluigi Guercia/AFP/GettyImages
Kisan kare dangi a mujami'u
Mujami'u ba su zama tudun na tsira ba. Kimanin mutane 4,000 maza da mata da kuma yara aka hallaka da adduna da wukake a mujami'ar Ntarama da ke kusa da birnin Kigali. Yau wannan mujami'a ta kasance daya daga cikin wuraren da ake tunawa da kisan kare dangi. Akwai kasusuwan kawuna da jikin mutane a bango da ke tunatar da abin da ya faru.
Hoto: epd
Rawar da Faransa ta taka
Faransa tana da hulda ta kut-da-kut da gwamnatin Hutu. Lokacin da sojojin Faransa suka shiga a watan Yuni, sojojin da tsagerun da suke da hannu wajen kisan kare dangi sun tsere zuwa kasar Zaire, wadda yanzu ake kira Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, tare da makamansu. Sun ci gaba da zama barazana ga Ruwanda.
Hoto: P.Guyot/AFP/GettyImages
Dafifin 'yan gudun hijira
Lokacin kisan kare dangin, miliyoyin 'yan Ruwanda 'yan Tutsi da Hutu sun tsere zuwa kasashen Tanzaniya da Zaire da kuma Yuganda. Miliyan biyu sun shiga Zaire kadai. Wadannan sun hada da tsaffin sojoji da wadanda suka shirya kisan kare dangi, inda suka kafa kungiyar Democratic Forces for the Liberation of Rwanda (FDLR), wadda take cin zarafin fararen hula a gabashin kasar Kwango.
Hoto: picture-alliance/dpa
Kama babban birni Kigali
Ranar 4 ga watan Yulin 1994 kungiyar Rwandan Patriotic Front (RPF) ta fara sintiri a yankin mujami'ar "Holy Family" a birnin Kigali. Zuwa lokacin da kungiyar ta karbe iko a mafi yawan kasar ta kawo karshen kisan kare dangi. Amma kungiyoyin fafutuka sun zargi 'yan tawayen da aika laifuka, sai dai babu wanda aka tuhuma har yanzu.
Hoto: Alexander Joe/AFP/GettyImages
Karshen kisan kare dangi
Ranar 18 ga watan Yulin 1994, shugaban RPF, Manjo-Janar Paul Kagame ya bayyana kawo karshen fada da dakarun gwamnati. 'Yan tawaye sun kwace babban birnin kasar da sauran manyan birane. Da farko sun saka gwamnatin riko. Daga bisani Paul Kagame ya zama shugaban Ruwanda a shekara ta 2000.
Hoto: Alexander Joe/AFP/GettyImages
Tabon karshe
An kwashe kimanin watanni uku ana kisan kare dangi. An yi amfani da adduna wajen yanka mutane. Mutane sun hallaka makwabta. Yara da tsofi ba su tsira ba, gawauwaki sun mamaye kan tituna da sauran sassan jikin mutane. Ba wadannan abubuwan ba ne kawai ke tunatar da mutane kisan kare dangin Ruwanda. Akwai kuma tunani.
Hoto: Timothy Kisambira
Hotuna 121 | 12
Shekaru 30 kenan Shugaba Kagame ya shafe yana mulkin kasar Ruwanda ta hanyar takaita 'yancin walwala tare kuma da murkushe 'yan adawar siyasa, lamarin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka saba jan hankali a kansa. Paul Kagame na ci gaba da zama a kan karagar mulki ne biyo bayan shiri mai cike da cece-kuce na sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar da ya yi a shekara ta 2015, inda aka mayar da wa'adin mulkin kasar zuwa shekaru biyar. Wannan lamarin ne dai, ya bayar da damar sake zabensa har zuwa shekara ta 2034. To amma, ta ya ya sabon wa'adin mulkin zai iya kyautata alakar Ruwanda da sauran kasashen duniya? Phil Clark da ke koyar da siyasar duniya a Kwalejin Nazarin Yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka a London, ya ce mai yiyuwa kasashen duniya da Ruwanda ke kulla kawance da su su iya yin tasiri a kan Kagame nan gaba. Ko ma dai ya za ta kasance a tagwayen zabukan na shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki dai, al'ummar kasar Ruwanda wanda kaso 65 cikin 100 ke da kasa da shekaru 30 da haihuwa Paul Kagame kadai suka sani a matsayin shugaba lamrin da ka iya kai su ga neman sauyin gwamnati. Amma di a halin yanzu, jam'iyyar FPR da shugabanta Kagame suna da farin jini sosai a tsakanin al'umma.