1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko sulhun Ruwanda da Kwango zai tabbata?

July 4, 2025

A daidai lokacin da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu, wani srahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa Kigali na da hannu a rikicin yankin gabashin Kwangon.

Amurka | Washington D.C. | 2025 | Donald Trump | Sulhu | Ruwanda | Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Amurka ta jagoranci sulhu tsakanin Ruwanda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Andrew Caballero-Reynolds/AFP/Getty Images

Sai dai rahoton ya nunar da cewa akwai sabanin ra'ayi a kan wasu batutuwa a tsakanin Ruwanda da madugun 'yan tawayen M23 Corneille Nangaa tun bayan da garuruwa da dama kamar Goma da Bukavu da kuma wasu biranen lardinan Kivu ta Arewa da Kivu ta Kudu suka kubce daga hannun Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, bayan gwabza fada na sama da watanni biyar. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da kwararrun Majalisar Dinkin Duniyar ke zargin Ruwanda da goyon bayan 'yan tawayen AFC-M23 ba, a yakin da suke yi da dakarun Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango wanda ya yi kamari a baya-bayan nan a gabashin kasar.

Karin Bayani: Yarjejeniya za ta taimaka a samu zaman lafiya Kwango?

Sai dai fadar mulki ta Kigali ta sha musanta wadannan zarge-zarge, duk kuwa da irin kwararan hujjojin da ake gabatarwa. Ga masaninin siyasar Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango Marius Mubalama a maimakon ci gaba da fitar da irin wadannan rahotannin, kamata ya yi Majalisar Dinkin Duniyar ta yi wa Ruwanda matsin lamba ta janye sojojinta kwata-kwata daga makwabciyar tata  musamman ma yankunan da ta mamaye. Da ma dai rahoton kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar da cewa, babbar manufar Ruwanda ita ce kwasar ma'adinan karkashin kasa a Kwango. Kuma Shugaba Paul Kagame ya gwammace ya hade gabashin Kwango da kasarsa, domin samun cikakkiyar damar cin gajiyar dimbin arzikin da ke wannan yanki.

Dalilan da ke sa rikicin gabashin Kwango ci gaba da kamari

03:21

This browser does not support the video element.

To amma a wani abu da masharhanta ke kira jirwaye me kama da wanka, Ruwandar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon a birnin Washington na Amurka a makon jiya, wadda ta shata kawo karshen wannan rikici. Sai dai a mahangar mai sharhi kan harkokin siyasa a kungiyar DYPOL Justin Kamilolo ya kama a yi taka-tsan-tsan, a game da wannan sulhu da Amurka ta jagoranci samarwa. Akwai dai sabanin manufa tsakanin Ruwanda da madugun 'yan tawayen AFC M23 Corneille Nangaa wanda ke da burin nausawa har zuwa Kinsasha fadar gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, domin tunbuke Shugaba Felix Tschisekedi daga kujerar mulki.

Karin Bayani: Saka hannu kan yarjejeniyar Kwango

Ruwanda ba ta goyi bayan wannan manufa, ba a cewar rahoton kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya. Dangane da haka ne ma wasu ke tunanin an mayar da madugun 'yan tawayen gefe, a sabuwar alkiblar da rikicin ya dosa. 'Yan tawayen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango dai, sun sake kunno kai a watan Nuwamba na 2021. Corneille Nangaa da ke zama tsohon shugaban Hukumar Zaben Kasar ya rikide zuwa dan tawaye a watan Disamba na 2023, inda ya fara jagorantar bangaren siyasa na tawayen da ake wa lakabi da AFC wato Alliance Fleuve Congo.