Ruwanda na shirin karbar wadanda Amurka za ta sallama
May 5, 2025
Ruwanda na cikin matakin farko na tattaunawa kan yadda za ta karbi baki 'yan Afirka da Amurka za ta tasa keyarsu zuwa gida.
Cikin 'yan shekarun nan dai, kasar ta Ruwanda ta kasance wani sansani da kasashen yammacin duniya ke amfani da ita wajen sauke mutanen da suka ji ba su bukatar zamansu a kasashen.
Kasar dai na yin hakan ne kuwa, duk da damuwar da take nunawa a gefe guda kan yadda hakan ke cin karo da dokoki na 'yancin bani Adama.
A shekara ta 2022 ma dai Ruwandar ta sanya hannu kan yarjejeniya da Burtaniya, inda ta karbi wasu dubban masu neman mafaka, kafin daga bisani kasar ta Burtaniya ta janye batun jim kadan bayan rantsar da Firaminista Keir Starmer.
Jim kadan bayan kama madafun iko cikin watan Janairu ne dai, Shugaba Donald Trump na Amurka ya kaddamar da aniyar share baki 'yan kasashen waje tare da kawo tsarin inda za a sake tsugunar da su.