Ruwanda ta kori 'yan gudun hijiran Burundi
April 1, 2018A cewar hukumomin na Kigali, wannan lamari ya wakana ne, sakamakon kin aminta da 'yan gudun hijiran na Burundi suka yi a yi musu rejista na zamani da kuma shausahawar rigakafi ta sabili da dalillai na addini a cewarsu. Wadannan 'yan gudun hijira na Burundi da ke a garin Gashora na Kudu maso gabashin kasar ta Ruwanda, an tisa keyarsu ne ya zuwa garin Gasenyi-Nemba da ke kan iyakar kasar ta Burundi da Ruwanda a cewar shaidun gani da ido.
Baki daya dai kimanin 'yan gudun hijirar kasar Burundi 2,523 ne suka yi gudun hijira ya zuwa Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, inda sakamakon fargabar mayar da su da karfin tuwo ya zuwa kasarsu ta Burundi, ta sanya suka yi ta sulalewa daga wannan kasa zuwa Ruwanda, inda suka nemi mafaka a ranar bakwai ga watan Maris da ya gabata.