Ruwanda ta musanta zargin kai hari Kwango
May 4, 2024Kasar Ruwanda ta musanta zargin da ake yiwa dakarunta na kai hari kan wani sasanin 'yan gudun hijira da ke Jamhuriyar Dimkradiyar Kwango, ta na mai zargin 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Kwango da kai harin. Mai magana da yawun gwamnatin Ruwanda, Yolande Makolo ya musanta zargin inda ya ce, dakarun RDF na aiki ne bisa kwarewa kuma ba za su iya taba kai hari kan 'yan gudun hijira ba.
Karin bayani: Katar na neman daidaita Kwango da Ruwanda
Kasar Amirka ta yi Allah wadai da harin na ranar Juma'ar da ta gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara. A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta fitar ta ce an kai hari ne daga wani yanki da karkashin ikon dakarun RDF. Sanarwar ta kuma kara da cewa, Amirka ta damu da yadda RDF da 'yan tawayen M23 ke kara fadada a gabashin Kwango.