1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda ta sallami manyan hafsoshin tsaronta

September 1, 2024

Manyan sojoji masu mukamin janar-janar da dama ne suka yi murabus wasu kuma aka sallame su a kasar Ruwanda a wani garambawul da ya shafi sama da mutum dubu guda a kasar.

Shugaba Paul Kagame na kasar Ruwanda
Shugaba Paul Kagame na kasar RuwandaHoto: Jean Bizimana/REUTERS

Shugaban kasr ta Ruwanda Paul Kagame, ya amince da murabus din Janar Jean Bosco Kazura da karin wasu sojoji dubu da 162 masu sauran mukamai.

Shi dai Janar Kazura, mai shekaru 62, kafin murabus din nasa, shi ne hafsan hafsoshin kasar, mukamin da ya rike tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.

Haka nan ma ya taba zama mai bai wa shugaba Kagamen shawara kan harkokin soja, sannan ya jagoranci rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Mali a tsakanin 2013 zuwa 2014.

Shi dai Shugaba Paul Kagame, ya zargi sojoji da dama ne da rashin da'a, abin kuma da ya sanya shi daukar matakin a cewarsa.