1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ruwanda ta yi abin yabo a rikicin kasar Mozambik

Usman Shehu Usman MA
August 20, 2021

Kasar Ruwanda ta yanke shawarar kai wa makwabciyarta Mozambik da ke fama da yaki dauki. Sojojin Ruwanda sun ma kwato iko da manyan biranen Mocímboa da Praia.

Mosambik | Soldaten in der Cabo Delgado Provinz
Guda dag cikin tankokin yaki da sojoji cikin shirin ko-ta-kwanaHoto: Marc Hoogsteyns/AP/picture alliance

Ba zato ne dai ‘yar mitsitsiyar kasar da ke gabar ruwan tekun Indiya, ta fada cikin rikicin ta’addanci. Kasar Mozambik wacce ta sha fama da yakin basasa, wannan rikici na ta’addanci sake fama ciwon da bai gama warkewa ba ne. Kawo yanzu shigar da kasar Ruwanda ta yi na agaza wa makobciyar tata, ta samu karbuwa daga al'uma.

Wannan nasarar da Ruwanda ta yi ta jawo babbar muhawara a Mozambik domin a girma da yawan al’umma kasar ta fi Ruwanda, abin da masana harkokin siyasar Afirka ke cewa su kansu nasarar sojan Ruwanda cikin karamin lokaci, ya sa su aza ayoyin tambaya kan karfin sojan kasarsu ta Mozambik.

Sojojin Ruwanda na sintiri a MozambikHoto: Marc Hoogsteyns/AP/picture alliance

Wannan rashin katabus da sojan Mozambik suka yi kan rikicin kasarsu, wata babbar barazana ce ga kasa mai 'yancin kai. Da ma dai kungiyar kasashen kudancin Afirka da aka sani da SADC, lokacin wani taronsu, sun yanke shawarar tura dakaru don yakar 'yan ta’adda a Mozambik.

 

To amma ko da kasar Afirka ta Kudu da ta fi karfin soja a Afirka, ba ta kai ga yin wani katabus ba, duk da cewa tun a awatan Yuni aka amince da tallafa wa Mozambik.

Al'ummar Mozambik fararen hula zuwa  kwamandojin soja, sun yi ta jinjina wa Ruwanda musamman yadda ko mummunan gumurzu ba cika samu ba har kuma ta yi galabar fatattakar 'yan ta’addan a cikin kasar Mozambik.