Ruwanda ta yi tir da matakan da Yamma kan rikicin Kwango
March 4, 2025
Ma'aikatar harkokin wajen Ruwanda ta soki lamarin kanada bayan da kasar ta yi Allah wadai da kasancewar sojojin Kigali a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango (DRC) tare da takaita harkokin kasuwanci da ita. A lokacin da take mayar da martani a cikin wata sanarwa, Ruwanda ta danganta matakan da Kanada ta dauka da wani abin kunya, kuma ta ce ba za su warware rikicin da ake fama da shi ba.
Tun daga karshen watan Janairu ne, kungiyar M23 da ke samun goyon bayan sojojin Ruwanda, ta mamaye manyan biranen Goma da Bukavu na gabashin Kwango. Sai dai Kanada ta ce kasancewar Ruwanda a makwabciyar kasa ya keta dokokin kasa da kasa.
Karin bayani: Mai ya hana kawo karshen rikicin Kwango?
Ita ma Jamus ta sanar ta dakatar da taimakon raya kasa da take bai wa Ruwanda saboda farmakin da kungiyar M23 ke kaiwa a gabashin Kwango. A nata bangaren, Birtaniya ta yanke shawarar dakatar da yawancin tallafin kudi da take bai wa Rwanda, yayin da Amurka ta kakaba wa tsohon ministan tsaro James Kabarebe takunkumin kudi, bisa zarginsa da goya wa kungiyar M23 baya.