Ruwanda za ta maka Burtaniya a Kotu
January 28, 2026
A shekarar 2022 ne, firanminstan Burtaniya, Boris Johson ya warware yarjejeniyar da kasar ta kulla da Ruwanda. Tun da fari karkashin yarjejeniyar, Ruwanda na shirin karbar 'yan gudun hijira marasa takardun shaidar zama daga Burtaniya a wani mataki na dakile kwararar bakin haure zuwa Birtaniyar. Duk da yake yarjejeniyar na cike da cece-kuce yayin da ta fuskanci kalubalen shari'a.
Karin bayani:Burtaniya za ta tura 'yan gudun hijira zuwa Ruwanda
A watan Nuwamba 2023, kotun kolin Burtaniya ta yanke hukuncin cewa yarjejeniyar ta sabawa doka a karkashin dokokin kasa da kasa. Firanminista Keir Starmer ya soke yarjejeniyar bayan ya hau kan karagar mulki a watan Yulin 2024.
Gwamnatin Landan ta ce ta biya Kigali fan miliyan 240 a wancan lokacin sai dai a yanzu Ruwandar na neman karin fan miliyan 50, kwatankwacin dala miliyan 68 a matsayin diyya bayan da Birtaniya ta gaza soke yarjejeniyar a hukumance.