Shugaba Diomaye Faye ya nada sabon firaministan Senegal
May 26, 2026
Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal ya nada Ahmadou Al Aminou Mohamed Lô, a matsayin sabon firaministan kasar kwana guda bayan raba gari abokin tafiyarsa na siyasa Ousmane Sonko.
Al Aminou Mohamed Lô da ke zaman kwararre a fannin tattalin arziki, ya jima yana rike da mukamai da dama ciki har da na ministan tsare-tsare a gwamnatin ta Faye da Sonko kafin su rabu.
Shugaban Senegal ya kori Firaminsta tare da rusa majalisar ministoci
Mohamed Lô, zai jagoranci majalisar ministocin kasar ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida da jam'iyyar Pastef maimulki Senegal ke kara dumi, sakamakon rarrabuwar kawunan da ake fuskanta mai nasaba da tsarin tattalin arziki tsakanin Sonko da Faxe, lamarin ya kai ga Shugaba Faye korar firaminsta daga mukamin.
Senegal: Sonko ya samu damar zama shugaban majalisa
Nan gaba kadan a yau ake sa ran majalisar dokokin kasar ta sake dawo da Ousmane Sonko a mukaminsa na dan majlaisa, kana kuma akwai yiwuwar ya nemi darewa kan kujerar shugabancin majalisar bayan da shugabanta kuma na hannun daman Sonko, El Malick Ndiaye, ya yi marabus.