1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saɓani tsakanin Isra'ila da Amirka akan nukiliyar Iran

September 16, 2012

Isra'ila ta buƙaci Amirka ta sanyawa Iran wa'adin jingine shirin nukiliyar ta ko kuma ta fuskanci matakin soji.

Prime Minister Benjamin Netanyahu of Israel speaks at the annual American Israel Public Affairs Committee (AIPAC) Policy Conference at the Washington Convention Center in Washington, D.C. on Monday, March 5, 2012..Credit: Ron Sachs / CNP
Hoto: picture-alliance/dpa

Firayi ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yayi gargaɗin cewar Iran za ta iya ƙera makaman nukiliya nan da watanni shidda ko bakwai masu zuwa, furucin da kuma ke zama ƙara matsin lamba ne ga buƙatar da ya gabatar wa shugaba Obama na Amirka ya ƙayyade wa mahukunta a birnin Tehran wa'adin da ba za su tsallaka ba game da shirin nukiliyar ko kuma ɗaukar matakin soji akansu, matakin da kuma shugaba Obama ya ƙi ɗauka, a wani abin da ake ganin zai ƙara zafafa taƙaddamar da ke tsakanin Amirka da Isra'lar da ke ƙawance da juna.

A lokacin da yake magana yayin wata hirar da aka yi da shi a gidan telebijin na NBC na Amirka, Netanyahu ya ce nan da tsakiyar shekara ta 2013, Iran za ta cimma kaso 90 cikin 100 na ƙarfin samar da bam na nukiliya. Akan haka ne ya buƙaci Amirka ta shata wa Iran layi tun a yanzu gabannin ƙurewar lokaci.

Wannan saɓanin da ya fito fili, da kuma shawarar da shugaba Obama ya yanke ta ƙin ganawa da Netanyahu nan gaba cikin wannan watan, sun sa jama'a sun gane irin rarrabuwar kawunan da ke tsakanin ƙasashen biyu a dai dai lokacin da Obama ke tsakiyar yaƙin neman zaɓen da zai gudana a cikin watan Nuwamban da ke tafe.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas