1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saɓani tsakanin Kudanci da arewacin Sudan akan Mai

January 23, 2012

Kudancin Sudan ta sanar da dakatar da aikin haƙar mai, tare da zargin makwabciyarta Sudan da kwace mata ɗanyen mai da kudinsa yakai dala miliyan 815

Michael Kauffmann Beschreibung MiRO8.jpg Deutsch: Erdölraffinerie MiRO, Werkteil 1 (ehem. DEA-Scholven) English: Oil refinery in Karlsruhe Datum 18. Juni 2005(2005-06-18) Quelle Michael Kauffmann Karlsruhe:Raffinerie
Matatar MaiHoto: cc-by-sa-Michael Kauffmann

Wannan batu dai na zama babbar barazan kan saɓanin da ke tsakanin ƙasashen biyu kan albarkatun Mai. A watan Yulin shekarar data gabata nedai, kudancin sudan din ta samu 'yancin kanta bisa ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarata 2005, wanda kuma ya kawo karshen yaƙin basasan shekaru masu yawa tsakanin kudanci da arewacin sudan din, sai dai ana cigaba da fuskantar saɓani dangane da rabon kudaɗen da ake samu daga albarkatun mai. Kudancin Sudan din dai na bukatar bututun mai daga arewaci da kuma rumbun ajiyar ɗanyan mai domin fitarwa zuwa ketare, sai dai sun gaza cimma yarjejeniya dangane da farashin da zasu biya, dangane da haka ne Khartum ta fara kwace man a matsayin kudinta. Tun daga ranar lahadi ne dai kudancin sudan ɗin ta fata tsayar da ayyukan hakar mai, wadda ake saran zata kammala nan da makonni biyu masu gabataowa, acewar kakakin gwamnati Barnaba Marial Banjamin. Rahotannin jami'ai dai na nuni da cewar kama daga watan Nuwanba, kudancin sudan din na haƙar gangan ɗanyan mai dubu 350, a kowace rana. Kuma kasar China babbar dillaliyar sayen mai daga wajen kasashen biyu.

Mawallafiya: Zainab Mohammed abubakar
Edita : Usman Shehu Usman