1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saɓani tsakanin NATO da Rasha

July 4, 2011

Rasha ta gargaɗi NATO dangane da makaman kariyar da take shirin ƙaddamarwa

Babban sakataren NATO Anders Fogh RasmussenHoto: dapd

Shirin amfani da wani tsarin makaman kariya da ƙungiyar ƙawance ta NATO ke so ta ƙaddamar, na zaman wata babbar barazana ga Rasha, kuma fadar mulkin Kremlin ta shawarce ta kada ta ƙaddamar da shirin ba tare da ta nemi shawarar ta ba. Sakataren harkokin wajen Rashan, Sergei Lavrov ya ce babu wata yarjejeniyar da zasu iya ƙullawa da ƙungiyar ƙawancen, -idan har ta cigaba da shirin nata zai zama wajibi su mayar da martani. Ministan ya yi wannan furucin ne a wani taron ƙolin na ƙungiyar NATO da hukumomin Rasha ke gudanarwa a wani wurin shaƙatawa da ke garin Sochi da ke kusa da tekun Baharum.

Babban sakataren NATO Anders Fogh Rasmussen ya amince da cewa akwai matsaloli dangane da makaman kariyar tsakanin ɓangarorin biyu amma ya yi amanar cewa za su cimma matsaya dangane da batun:

 " burin mu shine mu samar da tsari kala biyu yanda kowanne zai yi aiki da kansa domin cimma manufa ɗaya, waɗanda kuma zasu yi misayar batutuwar da zasu inganta tsaro a yankunan NATO da kuma na Rasha".

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi