1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saɓin ƙasashe membobin Majalisar Ɗinkin Dunia

October 16, 2007

Nan gaba a yau ne Majalisar Ɗinkin Dunia,zata zabi sabin ƙasashe 3 masu kujerun ƙayyaddaden lokaci a komitin Sulhu.

A na sa ran zaɓen Burkina Faso, Lybia, da Vietnam a matsayin sabin membobi na tsawan wa´adin shekara 2, wato 2008 da 2009.

Za su cenji ƙasashen Ghana, Congo, da Qatar a wannan kujeru.

Komitin Sulhu ya ƙunshi jimlar ƙasashe 15 membobi wanda su ka haɗa da 5 masu kujerun dindindin, wato Amrika France ,Britania, Russia da Sin.

A zaɓen sauran membobi n ko wace shekara 2, tsakanin ƙasashe 192 da Majalisar ta ƙunsa.

Saidai a halin da ake ciki, akwai mahaurta mai zafi, a game da wajibcin gudanar da kwaskawarima ga dokokin Majalisar Dinkin Dunia, tare da faɗaɗa komitin sulhu.