Sa'-in-sa tsakanin shugaban Najeriya da kafofin yaɗa labarai
August 28, 2013A wani abun da ke zaman ƙoƙarin kai wa na aiko sabon saƙo, gwamantin Tarrayar Najeriya ta ce ta cika tana shirin batsewa da hallaya irin ta 'yan addawar ƙasar da ke ƙoƙarin ganin bayanta ko ta halin ƙaƙa. Sannu a hankali dai ruwan na ƙara tsami haka shi ma gemun akuyar na daɗa girma a cikin Tarrayar Najeriya, da sannu a hankali adawa ke neman zama laifi a idanun masu ruwa da tsaki da mulkin ƙasar.
Rashin fahimtar juna tsakanin gwamnatin da 'yan jaridu
Babu dai tattaunawa a ɓangaren babban ministan shari'ar tarrayar Najeriya, da ya wakilici shugaban ƙasar a wajen taron lauyoyin ƙasar na shekara-shekara sannan kuma ya ce 'yan adawar ƙasar suna wuce makaɗi da rawa a ƙoƙarin kushe gwamnatin tasu. Duk da cewar dai bai fito filin wajen karatun mataki na gaba ba, tuni dai kalaman nasa suka fara tada hankula cikin ƙasar da a baya ta sha fama da mulikin kama karya, dama dai ya zuwa yanzu shugaban ya yi nisa a cikin kotu da wasu jerin 'yan jaridar da ya zarga da yi masa ƙazafi da kuma ya ce kotunan ƙasar ta Najeriya kawai ke kai ga raba su a ƙoƙari na ƙwatar hakkinsa.
Martanin 'yan adawa dangane da wannan taƙaddama
bTo sai dai kuma a faɗar senator Lawalli Shuaibu da ke zaman jigo a cikin jam'iyyar adawar ƙasar ta APC 'yancinsu ya fi gaban tawaya komai barazanar mahukuntan kasar da ya ce sun makaro.Ra'ayi a cikin mulkin jama'a ko kuma ƙoƙarin cin zarafi dai ana kallon sabon saƙon a ƙoƙari na taunar tsakuwa a ɓangaren gwamnatin da tuni ta yi nisa a cikin ƙoƙari na sake tabbatar da zarcewar shugaban da take daɗa tabbata yana shirin zarcewa a cikin mulkin nasa. Barrister Ahmed Aliyu Gulak dai na zaman mai ba da shawara kan batu na siyasa ga shugaban ƙasar, kuma a faɗarsa 'yan adawar ƙasar ba su da ta cewa in har ana batu na demokraɗiyya da ma mulki na gari.
Son zuciya cikin batu na adawa ko kuma ƙoƙarin ƙwatar mulki dai addawar ƙasar ta Najeriya ba ta bambanta da kowace addawa a ko'ina a duniya ba a cewar Malam Garba Umar Kari da ke zaman masani bisa harkoki na siyasa a ƙasar.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinaɗo Abdu Waba