1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sa-in-sa tsakanin sojojin Nijar da hadiman Bazoum

Gazali Abdou Tasawa MAB
July 31, 2023

Hukumomin mulkin sojin Nijar sun zargi Faransa da neman izinin wasu jami’an tsohuwar gwamnatin don kai hari da nufin kubutar da Mohamed Bazoum daga garkuwar da suka yi da shi. Sai dai jam’iyyar PNDS- Tarayya ta musanta.

Shugaban mulkin sojan Nijar janar Tchiani da hambararren shugaban kasa BazoumHoto: DW

A cikin sanarwa mai lamba 14 da majalisar mulkin soji ta CNSP ta fitar, ta zargi Hassoumi Massaoudou da ke zama ministan harkokin waje da Kanal Guire Midou babban kwamandan rundunar tsaro ta "Garde Nationale" da sanya hannu kan wata takarda da ke bai wa Faransa izinin kai farmaki a fadar shugaban kasa domin kwato Shugaba Mohamed Bazoum daga hannu masu garkuwa da shi.

Kakakin gwamnatin mulkin sojan Nijar Kanal Amadou AdramaneHoto: ORTN/REUTERS TV

Kakakin gwamnatin mulkin sojin Nijar kanal kamar dai yadda Amadou Adramane ya bayyana cewa:"A kokarin da take na samun hanyar da za ta ba ta damar yin amfani da karfin soja a Nijar, kasar Faransa da hadin gwiwar wasu ‘yan Nijar, ta gudanar da wani taro a hedikwatar rundunar sojoji ta "Garde Nationale" domin samun izini na siyasa da na soja da take bukata."

Sai dai yayin da take mayar da martini, jam'iyyar PNDS-Tarayya ta bakin kakakinta a nahiyar Turai Idrissa Wazir Dan Madaoua ta ce zargin ba shi da tushe da makama. Shi ma Lawael Sallaou Tsayyabou, shugaban kungiyar RODAHD da ke fafutikar kare dimoukradiyya cewa ya yi akwai alamar cewa sojojin da ke mulki sun rikice, kana akwai baraka a tsakaninsu.

Cibiyar jam'iyyar PNDS-tarayya a birnin YamaiHoto: DW/D. Köpp

Kame-kame na yawaita a PNDS-Tarayya

Ministan cikin gida Hamadou Adamou Soule ,ya nunar da cewa sabbin hukumomin mulkin soji na ci gaba da kamen ‘ya'yan jam'iyyar PNDS-Tarayya da abokanin kawancensu: A halin yanzu mutane kimanin 130 suka shiga hannu wadanda suka hada da Shugaban jam'iyyar na kasa Foumakoy Gado, da ministar ma'adanai Madam Ousseini Hadizatou Yacouba da Honnorable Kalla Moutari da ministan man fetur kana dan tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou, wato Maman Sani Mahamadou da ministan fasali Rabiou Abdou, da kuma ministan sufuri Alma Oumarou.