1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saadi Khaddafi ya ce zai koma Libiya

February 11, 2012

Gwamnatin Jamhuriya Nijar ta yi Allah wadai da kalaman Saadi Khadafi na cewa zai koma Libiya domin kifar da gwamnati.

ARCHIV - Der in das afrikanische Nachbarland Niger geflohene Gaddafi-Sohn Al-Saadi (Archivfoto vom 07.02.2005) soll versucht haben, mit den neuen libyschen Machthabern zu verhandeln. Die dem Übergangsrat nahe stehende Website «Al-Manara» meldete am Sonntag, der 38-Jährige habe über einen ehemaligen Geschäftspartner Kontakt zum lokalen Übergangsrat der Stadt Sintan aufgenommen. Die dortigen Verantwortlichen hätten es jedoch abgelehnt, mit ihm zu sprechen. EPA/MICK TSIKAS AUSTRALIA AND NEW ZEALAND OUT +++(c) dpa - Bildfunk+++
Saadi KhaddafiHoto: picture-alliance/dpa

Daya daga 'ya'yan tsofan shugaban kasar Libiya mirgayi Mohamar Khadafi, wato Saadi Khadafi wanda ya samau mafaka a jamhuriya Nijar, ya ce zai dawo kasar Libiya domin jagorantar yunkurin kifar da magabatan kasar da ya dangata da maciya amana.

Saadi Khaddafi ya wannan huruci a wata hira da yayi jiya da gidan talbajan na Al-Arabiya.

A cewar Saadi Kadafi a halin da ake ciki kashi 70 cikin dari na al'umar ba su gamsu da yadda ake gudanar da mulki.Ya danganta komitin koli na sojojin dake mulki a Libiya da 'yan fashi da makami, wanda kuma ya ce ko bade ko ba jima, al'umar Libiya zata kifar da su.

Tun dai watan Ogusta na shekara bara, Saadi Khadafi ya samu mafaka a Jamhuriya Nijar, kuma hukumomin kasar sun ce ba za su mika shi ba ga kotin kasa da kasa da ta bada sammacinsa.

A yayin da take maida martani gwamnatin Jamhuriya Nijar, ta bakin kakakinta Morou Amadou ta bayyana rashin amincewa da kalamomin na Saadi Khadafi.

Ita kuwa gwamnatin kasar Libiya jaddada kira ta yi, zuwa Jamhuriya Nijar ta mika mata Saddi Khadafi.Ministan harakokin wajen Libiya ya yi hannunka mai sanda ga hukumomin Nijar, tare da bayyana barazanar katsewar huldodi tsakanin kasashen biyu.

Sannan rahotani daga Libiya sun ce,bayan kalamomin na dan mirgayi Kaddafi wasu mutane sun kai farmaki ga ofishin jikadancin Nijar dake birnin Tripoli.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe