1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaJamus

Jamus: Sababbin tsare-tsaren zama dan kasa

Abdullahi Tanko Bala
December 8, 2023

Jamus ta zayyana tsare-tsare, domin bai wa wadanda suka zauna a kasar damar zama 'yan kasa. Daga ciki akwai rage yawan shekarun da ake bukata kafin zama dan kasa, daga takwas zuwa biyar da mallakar takardun kasashe biyu.

Takardun tafiya na Jamus
Takardun tafiya na JamusHoto: Maksym Yemelyanov/Zoonar/picture alliance

A karshen wannan shekarar ake sa ran zartas da sabuwar dokar zaama dan kasar, domin saukakawa da hanzarta shirin ba da izinin zama dan kasar da a baya ke da matukar wahala. Hakan ya zama wajibi saboda yawan takardun bukatar da ke karuwa, inda mutane da dama da ke zaune a kasar ke bukatar takardar zama Jamusawan. A birnin Berlin kadai an samu takardun bukata na mutane sama da dubu 16 a bara, ninkin adadin bukatar da aka samu a shekaru 10 da suka wuce. Kuma idan gwamnatin tarayya ta saukaka samun zama dan kasar, a nan gaba akwai yiwuwar wannan adadi zai karu. Daya daga cikin matakan saukaka shirin shi ne, rage wa'adin shekarun zama da ake bukata daga takwas zuwa biyar.

A halin da ake ciki 'yan asalin Siriya da dama sun cike takardun neman zama 'yan kasa, yanzu da yake sun cika sharuddan zama a Jamus na shekaru takwas. Ga likita Najat Alsamad an sha gwagwarmaya kuma  ba abu ne mai sauki ba, domin ta sha fama kafin samun a amince da takardunta na kwarewar aiki yayin da a waje guda kuma ta ke koyon sabon yare da kuma sajewa. Mutane da dama da ke zaune a Jamus suna neman zama 'yan kasa kuma takardun bukatar na taruwa a gaban hukumomi, sai dai kuma wasu ba za su so su yi watsi da kasashensu na asali ba. Ita ma Anamika Datta sai da ta hakura da kasarta ta asali, kuma wannan ya hana mutane da dama neman izinin zama 'yan kasar. Amma da wannan sabuwar doka, za a iya samun 'yancin zama 'yan kasashe biyu, kuma idan aka zartar da dokar za a hanzarta shirin zama dan kasar a shekara mai zuwa.