Saban Firaministan Tusiniya
February 22, 2013Shugaban ƙasar Tunisiya Moncef Marzouƙi ya amince da saban Firaministan da jam'iyar Ennahda ta naɗa.
Ennahda da ke riƙe da ragamar mulki a ƙasar Tunisiya, ta aiyanar da Ali Larayedh ministan cikin gida, a matsayin saban Firaminista,domin maye gurbin Hamadi Jibali da yayi murabus ranar Talata da ta gabata.Ali Larayedh mai shekaru 58 a duniya, ya yi gwagwarmaya a zamanin mulkin tsofan shugaban ƙasa Zin El-Abedine ben Ali, inda ya share shekaru 15 a kurkuku.
Shugaban Tunisiya ya umurci saban Firaministan ya girga gwamnati nan da kwanaki 14.
A halin yanzu 'yan Tunisiya sun zuba ido su ga yanayin sabuwar gwamnatin, da kuma kamun ludayinta, mussamman a ƙoƙarin magance matsalolin da suka wa ƙasar kanta, da kuma shimfiɗa tafarkin demokraɗiyya.
Tsofan Firmiyan Tunisiya Hamadi Jebali ya yi murabus dalilin da kasa cimma nasara girka sabuwar gwamnatin haɗin kan ƙasa, bayan kisan gillar da wasu 'yan bindiga suka yi wa Chokri Belaid, ɗaya daga cikin shugabanin adawar Tuniya, kisan kuma da ya jefa ƙasar cikin mummunan rikicin siyasa.
Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Zainab Mohammad Abubakar