Saban matakin Iran na mallakar nuklea
April 9, 2007A wani abu ,mai kama da ana magani kai na ƙaba,shugaba Mahamud Ahmadinedjad ya bayyana saban matakin da Iran ta cimma, a game da rikicin nukkea.
Shugaban ya ce, yanzu Iran, ta kai ga likkafa ta gaba, wajen sarafa Uranium, domin mallakar makamashin nuklea.
Ya gabatar da wannan sanarwa, a lokacin wani taro da ya jagoranta, a cibiyar sarafa Uranium ta Natanz, da ke tsakiyar ƙasa.
Ahmadu Nedjad , ya ƙalubalanci Majalisar Ɗinkin Dunia da Amurika, da ma ƙungiyar gamayar turai da su ka yanke hukunci saka wa Iran takunkumi a sakamakon wannan taƙƙadama.
Ya ƙara nanata cewa „babu gudu babu ja da baya“ a game da manufofin da Iran ta sa gaba.
Jim kaɗan bayan jawabin na sa, shugaba tawagar Iran, a tanttanawar nukleya, Ali Larijani, ya bayana yiwa fitar Iran, daga sahun ƙasashen da su ka rattaba hanu, a kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nuklea a dunia.
Ba da ɓata lokaci ba, ƙasar Amurika ta maida martani, ga kalamomin na shugaban ƙasar Iran.
A cewar kakakin fadar gwamnatin „White House“, yanzu yauni ya rataya a kan komitin sulhu, na Majalisar Ɗinkin Dunia,na ƙara tsuke takunkumin da ya ƙargamawa Iran.