Sabani a tsakanin jiga-jigan jam'iyyar PDP na neman jefa jam'iyyar cikin rudani
February 25, 2013Sannu a hankali dai tasirin jam'iyyar APC da babu zato ba tsamanni ta fito duniya na kara fitowa fili a cikin harkokin PDP da 'ya'yanta ke kara fuskantar zabuka na shekara ta 2015 cikin halin rudani da rashin tabbas.
PDP da tayi nisa a cikin gwagwarmayar mallakin ruhinta tsakanin gwamnonin kasar dake neman tabbatar da ikon su cikin jam'iyyar da kuma fadar shugaba Jonathan da ke neman tauyesu, yanzu haka kuma na fuskantar sabuwar barazanar raba kai a tsakanin gwamnoninta da wasunsu suka zauna suka ce sun kafa sabuwar kungiya ga gwamnonin PDP.
wani taron da ya samu halartar shi kansa shugaba Jonathan da mukarrabansa a fadar gwamanatin kasar ta Aso Rock sannan kuma da gwamnonin da ake kallon su na zaman na 'yan lelensa dai sun ce lokaci yayi da ita ma PDP za ta kama hanyar cin gashin kanta dan tabbatar da kungiyar ga gwamnoninta.
Shugaban sabuwar kungiyar gwamnonin PDP
Godswill Akpabio dai na zaman gwamanan jihar Akwa ibom kuma shugaban sabuwar kungiyar da tace ba ta fito domin takara da babbar kungiyar gwamnonin kasar ta Najeriya bane
" Yan uwana gwamnoni da shugabannin jam'iyyar mu sun zabe ni da murya guda domin shugabantar sabuwar kungiyar gwamnonin PDP. kungiyar mu ta zama daya daga cikin ginshikan jam'iyyar masu karfi. Gwamnonin PDP yanzu haka za su rika taro domin nazarin al'amuran da suka shafi jam'iyyar dama suka shafe mu kai tsaye. amma wannan ba yana nufin muna takara da kungiyar gwamnonin kasa ba saboda ita waccan tana lura da gaba daya al'amuran da suka shafi tarrayar Najeriya ne.amma wannan zai shafi muradun gwamnonin PDP ne kawai."
To sai dai kuma takara da kungiyar gwamnonin ko kuma bude sabon babin rikici dai sabuwar kungiyar ta zo ne kasa da tsawon 'yan awoyi da shirin zaben sababbin shugabannin kungiyar gwamnonin. Ana dai kallon sabuwar kungiyar a matsayin wani kokarin raba kan gwamnonin da yanzu haka kansu ke hade ga adawa da yunkuri na shugaba Jonathan na sake samun zabe a cikin jam'iyyar.
Sabuwar alkiblar jam'iyyar PDP
Fadar Aso Rock din dai a cewar majiyoyin taron na fatan amfani da sabon yanayi domin tabbatar da kawo karshen shugabancin dake kan mulki a kungiyar gwamnonin, shugabancin kuma da ke zaman kashi a wuyan fadar.
Ko bayan rikicin cikin gida na PDP sabuwar kungiyar da ta zo shekaru kusan 14 da bullar gwamnonin PDP na zaman wani martani ga barazanar 'yan adawar dake kara karfi dama samun gindin zama cikin harkokin kasar.
Tuni dai aka fara hasashen yiwuwar ficewar wasu gwamnonin PDP zuwa cikin sabuwar jam'iyyar APC ta gamin gambizar 'yan adawa. Abun kuma da a cewar Alhaji Bamanga Tukur dake zaman shugaban jam'iyyar wai ko ta ware ko ta wararye in ji Ungulun da ta taka mushen mota:
Da daren Litininnan (25. 02. 2013) ne dai ake sa ran mika rahoton wani kwamitin jam'iyyar dake neman mafita bayan gazawar fadar na tabbatar da nadin sabon shugabannin kwamiti na amintattu shekara kusan guda da saukar tsohon shugaban kwamitin Cif Olusegun Obasanjo ya kuma kai ga darewar jam'iyyar gida gida.
Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh