1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na adawa da abin da taron OPEC ya zartas

Abdourahamane Hassane
September 1, 2021

Wakilai na kasashen duniya masu arzikin man fetir na Kungiyar OPEC sun soma yin wani taro ta bidiyo domin kara yawan danyan fetir din da suke hakowa.

Erdölindustrie in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/STR

Ana sa ran wakilan za su sake tsaida ruwan miya a kan yarjejeniar da aka cimma a watan Yulin da ya gabata na hako gangar danyan man fetir miliyan biyar da rabi a kowacce rana. Sai dai mataimakin firaminstan Rasha Alexander Novak da ya halarci taron ya saka rudani, bayan da ya ce Rasha na iya kara addadin danyan man fetir da take hakowa fiye da yadda Kungiyar OPEC ta kayade: