Sabani tsakanin 'yan tawayen Siriya
July 2, 2014'Yan tawayen na gabashi da arewacin Siriyan sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar inda suka ce matukar jagororin adawar kasar basu taimaka musu wajen yakar 'yan kungiyar nan ta ISIL da ta addabi kasashen Siriyan da Iraqi ba to kuwa tabbas za su ajiye makamanszu tare da kuma janye mayakansu. Sanarwar dai ta baiwa 'yan adawar wa'adin mako guda kan su tabbatar da kammala samar da dakarun da zasu yaki 'yan kungiyar ISIL da kuma kayan agaji. 'yan tawayen sun kara da cewa a matsayin su na zaratan mayaka in har sauran kungiyoyin tawayen dake Siriyan da kuma gwamnatin rikon kwarya ta 'yan tawaye dake samun goyon baya daga kasashen yamma da kuma na Larabawa suka yi burus da bukatunsu to za su dauki matakin da suke ganin ya dace da su.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu