1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani ya hana kammala taro kan magance dumamar yanayi

December 8, 2012

An tsawaita taron Majalisar Dinkin Duniya kan damamar yanayi zuwa wannan Asabar

Hoto: BMU/ I. Strube

An tsawaita taron Majalisar Dinkin Duniya kan damamar yanayi zuwa wannan Asabar, yayin da mai daukan nauyin taron kasar Qatar ke neman shawo kan sabanin da ke tsakanin kasashe masu arziki da 'yan rabbana ka wadata mu.

An shafe sa'oi biyar ana neman samun matsaya da kasashe za su amince akai, bisa taron na birnin Doha, da ya dace a kammala a Jumma'ar da ta gabata, kuma akwai wakilai daga kusan kasashen duniya 200 da su ka halarci taron.

Abun da wakilan da ke halartar taron su ka amince na magance iska mai dumama yanayi, zai maye gurnin yarjejeniyar birnin Kyoto, kuma ana saran sabuwar yarjejeniyar ta fara aiki cikin shekara ta 2020, ana saran samun cikekken yarjejeniyar cikin shekara ta 2015.

Kasar ta Qatar ta nemi samun matsaya tsakanin kasashen, domin tabbatar da nasarar wannan taro na makonni biyu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas