1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Babu tabbaci kan tsare ma'aikatan asibitin al-Shifa a Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
November 23, 2023

Yayin da dakarun Isra'ila ke ci gaba da kai farmaki a kusa da asibitin al-Shifa da ke Gaza, babu tabbacin rahotanni da ke cewa sojojin Isra'ila sun tsare daraktan asibitin da wasu ma'aikatan lafiya.

Hoto: Hatem Ali/AP Photo/picture alliance

Kafofin yada labarai na kasa da kasa sun sha nakalto daraktan Mohammad Abu Salmiya game da halin da ake ciki a asibitin Al-Shifa, wurin da hankali ya koma saboda hare-haren da Isra'ila ke kai wa, bayan harin da kungiyar Hamas ta  kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

Sojojin Isra'ila da suka kai samame asibitin a makon da ya gabata, sun yi zargin cewa mayakan Hamas sun yi amfani da wani katafaren rami da ke karkashin ginin da ke Gaza wajen kai hare-hare. Zargin da Hamas da jami'an asibiti suka sha musantawa.